Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku bayani bisa dacewa da ranekun shahadar
Imam Hasan Askari (A.S) da kuma farkon Imamanci da wilayar Imam Asr (A.S), idanuwa
da zukatan ‘yan Shi’a sun nufi birnin Samarra da hubbaren Imamain Askaraini
(A.S.).
Birnin Samarra ya kasance yana da matsayi da daukaka a tarihin Musulunci da wayewarsa, kuma a yau yana daya daga cikin muhimman wuraren fadadawa da yada koyarwa Ahlul Baiti (AS) a Iraki da yankin Asiya da ma duniyar Musulunci.
“Bahman Dahestani” ya yi bayani kan matsayin birnin Samarra da haramin Imamain Askaraini (AS) a fagen siyasar Shi’a a wani rubutu da cikakken bayaninsa yake kamar haka;
Samarra ta zama hedkwatar halifancin Abbasiyawa a shekara ta 221 bayan hijira ta hannun Khalifan Abbasiyawa Mu’utasim Billah, kuma ita ce cibiyar gwamnati na tsawon kusan rabin karni, wanda iko da mulkin daular ya kai tun daga Tunisiya a arewacin Afirka zuwa tsakiyar Asiya.
Kamar yadda masana tarihi suka ce, a shekara ta 227 bayan hijira, lokacin da Mu’utasim Billah yana gab da rasuwa, birnin Samarra ta samu wadata da bunkasa ci gaba a wajen kyawawan fadoji da kyawawan gine-gine ta yadda ta yi gogayya da Bagadaza, wadda ake ganin ita ce hedkwatar wayewar Musulunci tsawon shekaru da dama. Kuma daukakar Samarra ta kasance har tsawon lokacin da halifofin Abbasiyawa suka sanya ta zama cibiyar wurin halifancinsu. Babban Masallacin Samarra, musamman babban hasumiya dinsa, wanda aka fi sani da Al-Malwiyya ko Pichghandar, wanda aka gina ta a zamanin Mutawakkul Abbasiyya, yana daya daga cikin fitattun gine-ginen da aka yi watsi da su a Samarra tun a wancan zamani. Bayan dawowar Abbasiyawa birnin Bagadaza ne aka kawo karshen bunkasar birnin Samarra kuma aka ruguza wadannan fadoji daya bayan daya, sai dai wannan kabarin da hubbaren limaman Askarain da ci gaba da tattaki da ziyara ta mabiya Ahlul Baiti (a.s) sun wanzu kiyayewar da su kai wa wannan wuri a tsawon karnoni da dama har zuwa yau ya sanya yankin a raye kuma a yanzu yana daya daga cikin garuruwan tarihi da al'adu na duniyar Musulunci kuma ya samu wayewa da tsaro a wannan yanki. A cikin 2007, UNESCO, ƙungiyar kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi rajistar wannan birni a cikin jerin abubuwan tarihi na duniya.
Hadisai da littafan Shi’a sun nuna cewa, gabatar da Mahadin da akai Alkawari da Imamancinsa, a rayuwar Imam Hasan Askari (a.s) a matsayin Imami magajin Imam Hasan Askari As an yi shi ne ga wasu kebantattun ‘yan Shi’a a Samarra kuma a gida da unguwar da Imami na 11 ne. Bugu da kari akan karantar da ‘Yan Shi’a a Samarra yanayin Gaiba da zamain Gaiba din abun ya waso a harsunan mutane gama gari da sauran masoya Ahlul Baiti (AS), ana kiran Samarra da gidan Imam Zaman As ne.
A cikin sanannen littafin Al-Tahzib daya daga cikin ingantattun madogara guda hudu na hadisin Shi’a, ya zo a cikin wani shahararren ruwaya na Imam Hasan Askari (a.s.) ya ce: “Abu Muhammad Al-Hasan bin Ali, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Kabari na a Sur Man Ra zi zamo Aminci ga ma’abota bangarori guda biyu”.
Wasu masu bincike da tafsirin hadisi suna ganin wannan ruwayar a matsayin abin da Imam Askari (a.s) ya yi nuni da tasirin kabarinsa wajen samar da tsaro da aminci ga ‘yan Shi’a da Ahlus-Sunnah da suka taru a kusa da hubbaren Samarra.
A lokacin da Amurka ta kai hari kasar Iraki a shekara ta 2003 ta kuma mamayar wannan kasa har zuwa faduwar Saddam, Iraki ta fada cikin wani yanayi na rashin tsaro da tashin hankali gami da hare-haren kungiyoyin takfiriyya masu dauke da makamai a kan 'yan Shi'a.
Mamaya da rugujewar tsarin siyasa da tsaro na kasar Iraki ya mayar da wannan kasa ta zama cibiyar kasantuwa da ci gaban kungiyoyin takfiriyya masu dauke da makamai, kuma kungiyar ta Al-Qaeda da rassanta sun gudanar da ayyuka da dama a fagen horar da sojoji da ayyukan soja a kan sojojin Amurka da 'yan Shi'a a lokaci guda. Baya ga sabanin akida da addini da akidar ‘yan Shi’a, wanda suke ga hakan ya ba su damar yin kisa, cikin yin kuskure sun dauki al’ummar Shi’ar Iraki da suke karakshin zaluncin gwamnatin Baath ta Sadam a shekaru da dama, tare da kasancewa tare da yan mamaya na Amurka da Turawa.
A yayin da aka samun sauyin mulki a kasar Iraki, bayan da 'yan Shi'a suka sami karfin iko, wasu sassa na al'ummar Sunni na kasar nan wadanda gwamnatin Baath ta Saddam ke marawa baya ko kuma 'yan wannan jam'iyya ne suka yanke shawarar daukar fansa kan 'yan Shi'a ta hanyar shiga ko taimakawa kungiyoyin takfiriyya masu alaka da Al-Qaeda. Sun dauki fuskantar yan shi’a a matsayin fuskantar mamayar Amurka.
Kungiyar ta'addanci ta Al-Qaeda, wacce ta kasance daya daga cikin dabaru da hanyoyin Amurka da kawancen sojojin kasashen yamma na kai hari da mamaye kasar Iraki; Bayan Afganistan, ta mayar da kasar Iraki wuri na biyu na kasancewarta mai karfi kuma ta yi amfani da shi wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan soji, kunar bakin wake da ta'addanci a karkashin sunaye daban-daban da rassa daban-daban.
Tada Bom a hubbaren limamain Askarain da ke Samarra, tashin bom da yyai sananin kashe shahidi Ayatullah Sayyid Muhammad Baqer Hakim, Tayarda Bom a lokacin Ashura a garuruwan Karbala da Kazemain, Tayarda Bom ginin majalisar dinkin duniya a Bagadaza, da aiwatar da hukuncin kisa kan sojoji da jami'an 'yan sanda sabuwar gwamnatin Iraki, da kuma fille kan 'yan kasar Iraki da na kasashen waje wani bangare ne kawai na ta'addancin kungiyoyin takfiriyya bayan kasancewar Amurka.
Abu Musab al-Zarqawi shugaban kungiyar Al-Qaeda a kasar Iraki yana daya daga cikin fitattun jigogin 'yan takfiriyya masu kishin jinin al'umma kuma dakaru masu fafutuka a wancan lokacin, wadanda a cikin faifan kaset din sauti anji maganarsa da ya ke ganin ya wajaba a kashe 'yan Shi'a baya ga kai farmaki da sojojin Amurka su ke yi kan 'yan Shi'a. Ya aminta da yada waanna manufa wajen ganin ankai hare-hare da dama a kan fararen hula da yankunan fararen hula na Shi'a.
A ranar Laraba, 23 ga watan Muharram, 2006, daidai da watana Isfand shekara ta 1384, wani mummunan fashewar bam ya faru da ya lalata hubbaren limamain Askarain tare da jefa duniyar Shi'a cikin kaduwa da juyayi.
Bayan wannan lamari mai ban mamaki, an sanar da zaman makoki a kasashen Iraki da Iran tare da rufe kasuwanni. Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sakon ta'aziyya ga wannan mummunan lamari na wulakanta haramin Imamain Askarain, inda ya sanar da zaman makoki na mako guda a kasar, tare da yin gargadi kan yiwuwar aiwatar da wani makirci na kasa da kasa a kan Shi'a da Sunna tare da bayyana cewa: "Ina ganin ya wajaba a yi kira da babbar murya ga al'ummar Iran da Iraki da sauran sassan duniya da su guji duk wani aiki da zai haifar da rikici da gaba tsakanin 'yan'uwa musulmi. Ko shakka babu akwai hannaye da za su tilasta wa ‘yan Shi’a su kai farmaki kan masallatai da wuraren da Ahlus-Sunnah ke mutuntawa amma ba su ba su wanna umarni ba. Domin duk wani aiki da za’a yi na taimakon manufofin makiya Musulunci da makiya al'ummar musulmi, doka ta haramta shi. A cikin wani sakon da ya fitar a shekara ta 2006, Ayatullah Khamenei, bayan wani harin da aka kai kan hubbaren Imam Hadi (a.s.) da Imam Askari (a.s.), ya tunatar da cewa: Hubbaren Askarain ya zamo abin girmamawa na tsawon karnoni a birnin Samarra ga Ahlus-Sunnah, kuma ba a taba barin wani ya ci zafarin sararinsa mai alfarma a kowane zamani ba. Yanzu, a lokacin mulkin mamaya, wannan shi ne karo na biyu da ake kai wannan hari na rashin kunya da laifi a wannan wuri mai tsarki. Masu mamaya na Iraki ba za su iya gujewa alhakin wannan babban laifi ba. Ya kamata 'yan'uwa Shi'a da Sunna na Iraki su yi taka tsantsan don kada su fada tarkon makircin makiya.
Mummunan harin da 'yan takfiriyya suka kai a hubbaren limaman Shi'a guda biyu da ba su ji ba ba su gani ba, ya haifar da fushin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin al'ummar Shi'a, kuma an bukaci tare da yunkuri na daukar fansa. Al'ummar yankin Samarra da ke lardin Salahad-Din da ke da mafi yawan al'ummar Sunna, su ne aka fara zargi da wannan mummunan lamari, kuma bayan shekaru uku na kisan gillar da kungiyoyin 'yan takfiri suka yi wa 'yan Shi'a da ba su ji ba ba su gani ba, da 'yan kasa da fararen hula da Al-Qaeda ko kungiyoyin da ke da alaka da ita suka aikata, da hadin kai da goyon bayan wasu yankunan Ahlus Sunna ko magoya bayan jam'iyyar Baath sun shirya fage mai yawa domin daukar fansa mai yawa daga 'yan Shi'ar tare da sanya Iraki a kan gaba domin aukuwar bakin yakin bangaranci da kabilanci mara iyaka.
A halin da ake ciki dai majalissar manyan Maraji’oi na Taqlid a Najaf Ashraf karkashin jagorancin Ayatullah Sistani ta kira wani taron sirri da na gaggawa cikin wani shiri na hikima ta hanyar fitar da fatawoyi da bayanai, tare da kira ga mabiya Shi'a masu fushi da bakin ciki da su kasance masu kamun kai da kuma hana shiga wani mummunan yanayi na cikin gida da na addini na yaki a Gabas ta Tsakiya.
Wadannan al'amura tare da jagorancin majalissar manyan Maraji’oi ta Najaf da goyon bayan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i ya sanya matasa da kungiyoyin Shi'a suke tunanin sadaukar da kai don tallafa wa hubbaren Askarain da samar da ingantaccen tsaro ga Samarra a matsayin cibiyar addini da al'adu a arewacin Bagadaza kuma tun daga wannan lokacin, ƙungiyoyin sa kai da horar da su ke da alhakin tabbatar da tsaron titina da birnin da kuma wurin ibada na tsawon shekaru da dama, kuma a yanzu Samarra, baya ga kasancewa ɗaya daga cikin garuruwa mafi aminci a tsakanin lardunan arewacin Iraki, su ne asali da kuma mafarin ci gaba da bunkasar kasashen Wannan yanki ta zama mai muhimmanci da kuma haifar da tsaro da kwanciyar hankali.
A halin da ake ciki kuma a cikin watan Yunin 2014 bayan harin mayakan ISIS tare da kwace birnin Mausul, sojojin wannan mugunyar takfiriyya sun isa kusa da birnin Samarra inda suke son su nufi zuwa Bagadaza da Karbala tare da haifar da tabarbarewar tsaron yankin gabas ta tsakiya baki daya, amma a wannan karon da taimakon Imamain Askarain da gwagwarmayar masu kare haramin yunkurinsu ya durkushe a wajen Samarra, kuma hakan bai ci gaba ba, wanda ya bayyana ma kowa da kowa irin yanayin matsayi da siyasar da ake akwai a cikin lamarin.