Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku
cewa: An gudanar da taron kasa da kasa mai taken: "Gwagwarmaya, Tabbatuwa
Da Farkawa" hadi da taron yada
labarai na "Karbala Dariqul-Aqsa", wanda ya samu halartar masana
addini, masu fafutukar al'adu da yada labarai daga kasashen duniya daban-daban.
An gudanar da taron a ranar Asabar da yamma - 24 ga watan Agusta 2024 a birnin
Karbala Madaukakiya bisa himma da daunkar nauyin majalissar Ahlul Baiti (AS) ta
duniya.
Ayatullah Ramazani, Babban Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya, “Shaikh Ibrahim Zakzaky", Babban Shugaban Harkar Musulunci a Najeriya da Hujjatul Islam "Raja Nasir Abbas Jafari", Shugaban Majalisar Hadin Kan Musulmi ta Pakistan” ne su ka zamo masu jawabi na musamman na wannan taro.
A wannan taron kasa da kasa mai taken: "Gwagwarmaya, Tabbatuwa Da Farkawa" an fara da ne da Karatun ayoyi da dama daga cikin kur'ani mai tsarki sannan kuma aka karanta ziyarar Arba'in ta daren Arba'in Imam Husaini (AS).
Arba'in Cigaba Ce Na Tsarin Gwagwarmaya
A yayin da yake tarbar baki na kasashen duniya da suka halarci taron, Ayatullah Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya ya bayyana cewa: Arba'in lamari ne na mutumtaka da ruhiyya kuma yana iya kafa turbar sabuwar wayewar Musulunci ga musulmi da dukkan bil'adama.
Malamin ya jaddada muhimmancin rawar da malaman addini suke da shi wajen hana gurbata taron Ashura yana mai cewa: Arba'in tana koyar da ingantaccen babban nasara ne. Idan da Karbala bata kasance ba, da ba a samu alamar Musulunci ba. Addinin Musulunci mafarinsa Annabi Muhammad ne kuma wanzursa Da Tasirin Imam Husaini As ne.
Ayatullah Ramezani ya gabatar da jahilcin al'umma a matsayin musabbabin canjawar abubuwa masu muhimmanci zuwa kishiyantar juna, ya kuma bayyana cewa: Jahilci yana kawar da hakikanin abin da ke gudanar da rayuwa daga mutum. Imam Sadik, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: بَذَلَ مُهجَتَهُ فِیکَ لِیَسْتَنْقِذَ عِبادَکَ مِنَ الجَهالَهِ وَ حِیرَةِ الضَّلالَه؛” “Ima Husain As ya sadaukar da ruhinsa domin tseratar da bayinka daga jahilci da rudani da bata; Wato Imam Husaini (AS) ya bayarda ransa ne domin ceto al'umma daga jahilci da rashin sani da bata.
Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya dauki duniyar Musulunci a matsayin mai gaba da gaba da kafirci yana mai cewa: A yau duk wanda ya ba da labarin Arba'in dole ne ya yi magana kan zaluncin da ake yi wa mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza. Arbaeen (AS) na Husaini (AS) ci gaba ce ga tsarin gwagwarmaya kuma tana kan tafarkinta.
Yin Koyi Da Salon Rayuwar Imam Husaini (A.S.)
Babban Shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, “Sheikh Ibrahim Zakzaky", a lokacin da yake gabatar da ta'aziyyar zagayowar Arbaeen Husaini (AS) ya jaddada muhimmancin yin koyi da salon rayuwar Imam Husaini (AS) kuma ya dauki nuna goyon baya ga mutanen Gaza da ake zalunta a halin yanzu ci gaba ne bisa tafarkin Aba Abdullahil-Husain (AS).
A ci gaba da halartar ma'aikatan haramin Razawi (a.s) mai tsarki, tutar haramin Imam Rida (a.s) ta kasance babban bakon taron, wadanda suka halarta sun yi gaisuwar jinjinawa gareta da kuma rera wake-wake. Da ke cewa "Habibi ya Hussain (a), Habibi ya Reza (a)".
Imam Hussain (AS), Ne Shugaban ‘Yantattun Duniya
Shugaban majalisar hadin kan musulmi ta kasar Pakistan Hujjatul Islam “Raja Nasir Abbas Jafari” ya bayyana halin da Palastinu da aka mamaye a halin yanzu da kuma muhimmancin hada kan musulmin duniya, inda ya gabatar da Imam Hussain (AS) a matsayin shugaba na mutanen duniya masu 'yanci.
Har ila yau, a cikin jerin jajantawa da nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da ake zalunta, an raba tutocin Falasdinu a tsakanin mahalarta taron inda mahalarta taron suka nuna rashin jin dadinsu da laifukan da gwamnatin sahyoniyawa ke aikatawa a Gaza ta hanyar rera taken "Labaik Ya Palastinu, Labbaik Ya Gazza".
Dr. "Akmal Kamel" daga Indonesia, Hujjatul Islam "Sayyidd Alireza Razawi" daga Ingila, Maulwi "Bahruddin Jozjani" daga Afghanistan da "Hermit Sink" daga Pakistan suma sun halarci mai taken: "Gwagwarmaya, Tabbatuwa Da Farkawa" tare da gabatar da nasu bayanan.
Tattaunawar da wasu daga cikin mahalarta taron da masu fafutukar al'adu da yada labarai suka yi da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na Abna game da batutuwan da suka shafi ranar Musulunci ta duniya da kuma wajabcin bayar da kulawa ta musamman ga kafofin watsa labarai kan wannan gagarumin taron na Arba'in na Husaini na daya daga cikin abubuwan da suka gudana a wannan taro.
A karshen wannan taro da kuma bayan waken ta'aziyyar musibar Aba Abdullahil-Husain (a.s) an bayar da dama ga duk wadanda suka halarci wannan taro don bayyanawa da nuna samun albarkaci ga Imam Rauf (a.s.) a daren Arbaeen Husaini (a.s.) sun samu albarkacin tutar Imam Riza (a.s.).





