Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku cewa: Bayan shahadar mai girma mujahid, Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a cikin sakonsa, yayin da yake jajantawa akan shahadar wannan jajirtaccen shugaba kuma fitaccen mujahid. ya jaddada wa al'ummar musulmi, da kungiyar gwagwarmaya da kuma al'ummar Palastinu maɗaukakiya cewa: gwamnatin sahyoniya mai aikata zalunci da 'yan ta'adda da aiwatar da wannan mataki ta tanadarwa da kanta tsattsauran hukunci kuma muna ganin Wajibinmu ne daukar fansarsa wanda ya yi shahada a cikin kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran hakkinmu ne
Nassin sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne kamar haka;
بسم الله الرحمن الرحیم
انا لله و انا الیه راجعون
ملت عزیز ایران!
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Daga Allah Mu Ke Kuma Gareshi Mu Ke Komawa
Ya ku al'ummar Iran!
Jarumi kuma fitaccen jagoran mujahidan Falasdinu, Isma'il Haniyeh ya koma ga Allah a daren jiya, hakan ya sanya babban fagen gwagwarmaya cikin juyayi. Gwamnatin sahyoniya mai laifi da ta'addanci ta shahadantar da babban bakonmu a gidanmu tare da sanya mu cikin bakin ciki, amma kuma da aikata hakan ta shirya wa kanta hukunci mai tsanani.
Shahidi Haniyyah ya tafiyar da rayuwarsa mai daraja ta tsawon shekaru da dama a fagen gwagwarmaya mai daraja kuma ya kasance a shirye don yin shahada, ya sadaukar da ‘ya’yansa da al’ummarsa ta haka. Ba ya tsoron zama shahidi a tafarkin Allah da kubutar da bayin Allah, amma muna ganin hakkinmu ne mu nemi jininsa a cikin wannan lamari mai daci da tsanani da ya faru a cikin Jamhuriyar Musulunci.
Ina mika ta'aziyyata ga al'ummar musulmi, ga bangaren gwagwarmaya, al'ummar Palastinu masu jaruntaka da alfahari, musamman ma iyalai da wadanda suka yi saura da rayukansu na Shahidi Haniyyah da daya daga cikin mataimakansa da suka yi shahada tare da shi, ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya dakaka darajarsu.
Sayyid Ali Khamenei
10 Murdad, 1403,
25 ga Muharram, 1446