10 Yuli 2024 - 08:04
Abubuwan Da Suka Faru A Ranar Hudu Ga Muharram, 61 Hijiriyya

Bayan cikar rana ta uku ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira, a rana ta hudu, Ubaidullah bin Ziyad ya tara mutanen Kufa a masallaci ya gabatar da jawabi, sannan ya kwadaitar da jama'a da su halarci yakar Imam Hussaini (AS).

Bayan cikar rana ta uku ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira, a rana ta hudu, Ubaidullah bin Ziyad ya tara mutanen Kufa a masallaci ya gabatar da jawabi, sannan ya kwadaitar da jama'a da su halarci yakar Imam Hussaini (AS).

Jawabin Ubaidullah bn Ziyad akan Imam Hussaini (a.s) a masallacin Kufa.

A wannan rana Ubaidullah bin Ziyad ya tara mutane a masallacin Kufa, ya hau kan minbari ya ce: Ya ku mutane! Kun gwada iyalan Abu Sufyan kun san su yadda su ke! Kuma kun san Yazid, wanda yake da kyakykyawan dabi’a da hali! Kuma yana fifita talakawansa! Kuma kyautarsa ​​ta cancanta! Haka kuma mahaifinsa Mu'awiya ya kasance a zamaninsa, shi ma dansa Yazidu yana girmama talakawansa a bayansa!

Kuma yanzu Yazid ya umarceni da in kara kaso mai gwabi daga kyautuka kuma ya aiko min da kudi in raba muku, in tura ku yaki ga makiyinsa Husaini! Don haka ku ji wannan bayani, ku yi biyayya gareshi.

Sannan ya sauko daga kan mimbari ya bawa jama'a kyauta mai yawa da taimakon Umar bin Sa'ad ya aika da mutane zuwa yakar Husaini (a.s) Sannan kuma ya ba da umarni a bawa mutanen Sham kyauta ta musamman ya kuma umurce su da su kwadaitar da mutane da zaburantar da su a ko'ina cikin birnin cewa su zamo cikin shirin tafiya yaki...