Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) na kasa da kasa - ABNA ya habarta cewa, Ayatullah Muhammad Jawad Fazil Lankarani mamba a jami'ar Mudarrisin ta Qum ya bayyana a wurin taron tunawa da wafatin Imam Khumaini (RA) da kuma yunkurin juyin 15 Khordad: waki'ar juyin juya halin Musulunci ba wani lamari ne na yau da kullum ba ne kamar yadda sauran sauran al'amura da suke faruwa ba ace wata rana kawai ya faru kwatsam a tarihi kuma wata rana ace an kawar da shi, sai dai hujjoji sun nuna cewa juyin juya halin Musulunci wata falala ce ta musamman da Allah ya yi wa bil'adama da ya faru a Iran.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da ainihin akidar juyin juya halin Musulunci, ya jaddada cewa: Tun da farko juyin juya halin Musulunci ya yanke sa hannun baki daga wannan kasa, kuma a yanzu muna shaida cikakkiyar 'yancin kai na siyasa.
Ayatullah Fazil Lankarani ya ce juyin juya halin Musulunci na Iran ya haifar da farkawa ta gaba daya a duniya baki daya, Ayatullah Fazil Lankarani ya kara da cewa: A yau muna shaida irin koma bayan da kasar Isra'ila ta samu da kuma koma bayan mafi girman karfin Amurka, kuma ra'ayin jama'a ba zai iya rufe ido akan haka ba.
Babban malamin mai koyarwa a jami'o'in Qum yana ganin nasarorin da juyin juya halin Musulunci ya samu a matsayin falalar Ubangiji ta musamman da kuma hikima da shiriyarwar Imam da Jagora inda ya kara da cewa: Wadannan akidu ba za su tabbata ba ba tare da sadaukarwar mujahidai da tsarkakakken jinin shahidai da kasantuwar al'umma a kan fage wadanda su ne ginshikan juyin juya halin Musulunci na Iran.
Ayatullah Fazil Lankarani a yayin da yake bayani kan matsayin al'ummar Iran da kuma daidaikun mutane a cikin wannan gagarumin lamari na juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Wajibi ne kowa da kowa a Iran ko a wajen Iran ya ayyana matsayinsa a wannan yunkuri na duniya; A bisa riwayoyin A'immah Aɗhar (AS) juyin juya halin Musulunci zai kasance ginshikin wani gagarumin yunkuri na duniya; Tabbas wannan shara fage ba yana nufin ganin bayyana a kwanaki ko shekarun da suka gabata ba ne, sai dai wannan bangare na tarihi yana da tasiri a zamanin bayyana da kuma gwamnatin duniya.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da tasirin kasa da kasa na juyin juya halin Musulunci da kuma yadda wadannan ayyuka da albarka suke ci gaba da yaduwa, mamba a makarantar Qum ya jaddada cewa: Wajibi ne mu nemo Matsayinmu na tarihi, mu ga irin gudunmawar da muke son samu a addinance, saboda Juyin Musulunci yunkuri ne na addini tun daga Adam (a.s) da annabawa na farko zuwa Annabi na karshe da imamai ma'asumai (a.s) da Ashura da sauransu, kuma wannan yunkuri ne guda daya.
Ya bayyana cewa Allah ya halicci addini domin dan Adam ya zama cikakke, ya ce: Tun daga annabawa da imamai zuwa malamai da mujahidai da malaman fikihu da sauransu kowa ya bayar da gudunmawa sosai wajen wanzuwa da karfafa addini, don haka idan muna son addinin Musulunci yaci gaba da yaduwa Ako yaushe a duniya a yau, kuma a yadu a kowace rana, wajibi ne mu kiyaye wannan juyi da dukkan karfinmu, domin kuwa duk wata barna da zata samu juyin juya halin Musulunci to zai hana motsin addinin Musulunci; Tabbas nufin Allah shi ne sannu a hankali a hankali addinin Allah ya samu karɓuwa ga jama'ar duniya, wanda kuma tunanin al'umma zai fi sanin tauhidi da Alkur'ani ta hakan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da amsa tambayoyin da mutum zai yi a gaban Ubangiji dangane da yunkurin addini na tarihi, ya kara da cewa: Kimar dan Adam tana kayyade a cikin irin wadannan abubuwa, don haka wajibi ne mu samu namu irin gudummuwarmu da rawar da muka iya takawa da kuma fitar da abin da za mu iya a wannan fage.
Haka nan kuma ya yi ishara da ayar:
«إِنَّ اللّهَ لاَ یُغَیِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّى یُغَیِّرُواْ مَا بِأَنْفُسِهِمْ»
" Lalle Allahu ba ya canja abin da ke ga mutane har sai sun canza da kansu" ya kuma tunatar da cewa: Sunnar ce ta Ubangiji cewa canza rayuwar bil'adama ta hannunsu yake faruwa, don haka idan muna neman gwamnati mai adalci, Allah zai yi mana gamdakatar da samun hakan kuma idan muka nemi gwamnati marar adalci to gwamnatin rashin adalci zata ta zo.
Ayatullah Fazil Lankarani ya dauki juyin juya halin Musulunci a matsayin amana inda ya ce: Tilas ne a isar da juyin juya halin Musulunci ga al'ummomin da za su zo nan gaba tare da dukkan siffofinsa na hakika.
-------------
karshen sakon