26 Mayu 2024 - 15:23
Cikakken Matanin Sakon Ta'aziyyar Da Shekh Ibarhim Al-Zakzaky {H} Ya Aikewa Al'ummar Iran Na Shahadar Shugaban Kasar Da Abokan Tafiyarsa

Farko zan fara da yin ta'aziyya ga Sahibul Asri Wazzaman wanda shi ke gudanar da al'amuran wannan al'umma, kuma wadannna manyan mataimakansa ne, ainhin ya rasa su adaidai wannan lokaci, da kuma ga Sayyid Qa'id Hafizahullah, wanda harma wasu suka rinka cewa dan Allah mu yi Addu'ah ga Sayyid Qa'id Hafizahullah, saboda ainahin gaskiya lalla an jarabce shi da damuwa babba na rashin babban jigo koma in ce manyan jiga-jigai na mataimakansa masu Iklasi.

Cikakken Matanin Sakon Ta'aziyyar Da Shekh Ibarhim Al-Zakzaky {H} Ya Aikewa Al'ummar Iran Na Shahadar Shugaban Kasar Da Abokan Tafiyarsa

Assalamu Alaikum Warahmatullah

Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji'un! Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji'un!! Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji'un!!!

Ah! Ina son in yi magana ne dangane da wannan musiba da ta same mu adaidai wannan lokaci, na rashin wadannan bayin Allah, Shugaban kasar Jamhuriyyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi, da wazirinsa na harkokin kasashen waje, Agaye Husain Amir Abdullahiyan, da limamin Tabriz kuma wakilin Sayyid Qa'id a lardin gabashin Azarbaijan, da gwamnan gabashin Azaibaijan, da wadanda suke tare da su, a abunda zamu iya ce masa wata Karisa mummuna da ta aukua Helkwaftan da suke tafe, wanda aka rasa su gaba dayansu.

wanna ya auku a daidai lokacin da muke cikin bukin tunawa da ranar haihuwar Imam Ridha As, ranar 11 ga watan Zulqa'adah, muna cikin wannan buku sai kawai ya dawo ya zo mana cewa ainahin ga halin da ake ciki, ba'a ga jirgin shugaban kasa ba, to wannan sai ya sa ainahin wannan zama namu na buku ya koma jaje, aka fara aka koma ana addu'o'i, wanda mu anan hakan nan duka akaita addu'o'i, mu kai ta bin abubuwan da suke faruwa dakika bayan dakika, ainahin idanunmu ba su iya barci ba a wannan dare, sai zamo labari marar dadi yazo mana na cewa ba'a samu ko dayansu da rai ba, wannan ya kadamu sosai ya girgizamu sosai ya samu cikin matsananncin bakinciki da dimuwa, mun girgiza sosai, kuma kalmomi ba zasu iya bayyana irin kaduwarmu da alhininmu da bakincikinmu a wannan rana ba jin irin wannan abun ya faru.

Farko zan fara da yin ta'aziyya ga Sahibul Asri Wazzaman wanda shi ke gudanar da al'amuran wannan al'umma, kuma wadannna manyan mataimakansa ne, ainhin ya rasa su adaidai wannan lokaci, da kuma ga Sayyid Qa'id Hafizahullah, wanda harma wasu suka rinka cewa dan Allah mu yi Addu'ah ga Sayyid Qa'id Hafizahullah, saboda ainahin gaskiya lalla an jarabce shi da damuwa babba na rashin babban jigo koma in ce manyan jiga-jigai na mataimakansa masu Iklasi.

Kuma muna Ta'aziyyarmu ga ainhin iyalan wa'yan nan bayin Allah da duk akai masu mufaja'a da rashin masoya bagtatan, da kuma musamman Al'umman Jamhuriyar Musulunci ta Iran da daukacin Al'ummar Musulmi baki daya, musamma ma 'yan gwagwarmaya na muslunci a Falasdin da Labnan da Irak da Suriya da Yamen da sauran sassa na duniyar Musulmi dama daukacin Bil Adama baki daya. wanna gaskiya babban rashi ne, muna jajatama muna taya duk cikanmu jajen akan wannan abun da ya faru.