Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Hakazalika, za a yi jana'izar gawar Shahid Dr. Amir Abdollahian da misalin karfe 11:00 na safe a wannan rana ta Alhamis 23 ga watan Mayu a hubbaren Sayyidina Shah Abdul Azim Hasani (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ke Shahr Ray Tehran.
21 Mayu 2024 - 17:55
Lambar labari: 1460153
Za a yi taron bankwana da mujahidin ministan harkokin waje na juyin juya halin Musulunci, Shahid Husain AmirAbdollahian, da misalin karfe 9:00 na safe a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu a Dandali Mashk na ma'aikatar harkokin wajen kasar (kofar shiga titin Ferdowsi).