10 Agusta 2023 - 13:27
Ayatullahi Ramdhani: Sabon Shirin Makiya Shi Ne Nesantar Da Matasa Tare Da Cire Shari'ar Musulunci Daga Garesu

Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ya Gana Da Amirul Hajj na Musulman kasar Thailand: Sabon Shirin Masu Girman Kai Shi Ne Cirewa Tare Da Kwace Shari'ar Musulunci Daga Hannun Matasa.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Amirul Hajj na Musulman kasar Thailand da wakilan Sheikhul Islam na kasar sun gana da babban sakataren Majalissar Ahlul Baiti (a.s.) ) Ta Duniya a dakin taron Majalissar da ke Tehran a ranar Litinin 7 ga Agusta 2023.

Ayatullah Ramadani: Alhamdulillah, musulmin kasar Thailand suna da yanayi mai kyau; amma mafi muhimmanci shi ne kula da wannan yanayin da gudanar da shi yadda ya kamata, kuma shugabannin musulmi su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A cikin wannan ganawa, Ayatullah Riza Ramezani a lokacin da yake karbar baki, ya yi ishara da wurin aikin Hajji a Musulunci inda ya bayyana cewa: A wata ruwayar Imam Bakir (AS) Hajji na daya daga cikin rukunan da Musulunci ya ginu a kansu. Aikin Hajji na samar da alakar kasa da kasa tsakanin kasashen musulmi domin yin mu'amala da warware matsaloli.

Ya ci gaba da cewa: Musulmai sukan taru a Mina inda za su iya kulla mafi kyawu mu'amala a tsakaninsu, amma makiyan musulmi ba sa son wannan taro kuma ba sa barin hadin kan musulmi ya tabbata.

Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ce game da muhimmancin hadin kai da wajabcin hadin kai a tsakanin musulmi: Ra'ayinmu game da musulmi ya dogara ne da hadisin "Al-Mu'min Akhul-Mu'min" a kan batu na soyayya da kuma tsarin hadin gwiwa da hadin kai. A daya bangaren kuma hadin kan al’ummar musulmi imani ne da gamsuwarmu da nusarwa ta dindindin ba ta wucin-gadi na dan kankanin lokaci ba.

Ya kuma jaddada cewa: A yau ya kamata musulmi da dukkan al'ummominsu da gwamnatocinsu su yi amfani da damarsu ta al'adu da zamantakewa da siyasa fiye da a baya. Haduwar wadannan madafun iko yana nuna irin girma da karfin da musulmi suke da shi a kan masu girman kai. Imam Khumaini (R.A) ya ce: "Idan Musulmi suka hadu, kowannensu ya zuba guga daya na ruwa a kan Isra'ila, sai ya yi ambaliya ruwa ta kawar da ita." Mun yi imani da cewa da musulmi za su kasance tare a fagen tattalin arziki, da sun kasance mafi girman karfin tattalin arziki. Haka nan kuma ya kamata dukkan malaman addini da musulmi su kiyaye kada makiya su shigo cikin al’ummarmu ta kowace hanya.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Ramezani ya ce dangane da manufofin Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya: Majalisar tana kokarin raya hankali da ruhi da adalci a duniya tare da bin wannan adabi, na hankali da a aikace a dukkan fadin duniya a dukkan fagagen aikinsa.

A yayin da yake bayyana nasarori da ayyukan Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya, ya bayyana cewa: Kundin bayanai na Wiki Shia yana aiki a cikin harsuna 22, kuma kamfanin dillancin labarai na Abna yana aiki a cikin harsuna 26. Kasashe 29 ne ke karatu a jami'ar kasa da kasa ta Ahlul Bayt As kuma mun buga ayyukan bincike guda 2000 a cikin harsuna 58.

Babban magatakardar majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya ya bayyana cewa dole ne a isar da addinin Musulunci ga musulmi ba tare da gurbacewa ba, ba tare da wuce gona da iri ba, yana mai cewa: makiya suna neman raba kan musulmi ne da sanya su yi fada da juna, inda a karshe. A shekaru uku na na baya bayan nan da suka wuce, sun aiwatar da kisan kai a duniya, an yi hakan ne da sunan Musulunci a kuma tsakanin Musulmi.

Ya ambaci laifuffukan da ‘yan takfiri suka aikata a duniyar Musulunci, ya kuma ci gaba da cewa: ‘Yan ISIS da takfiriyya sun fille kawunan mutane da sunan Musulunci suna masu Kabbara da Hailala, alhali ayyukansu ba shi da alaka da Musulunci. Inda ya kamata mu an baci tare da tunawa da jagororin kasashen musulmi da fagen gwagwarmaya, wadanda suka kawar da sharrinsu daga musulmi.

Farfesan na manyan jami'o'in makarantun Hauza ya bayyana cewa ya kamata kungiyoyin addini da na mazhabobi da su gabatar da addinin Musulunci cikakkensa, daidai a zurfinsa, sannan ya kara da cewa: Sabon shirin masu girman kai shi ne cirewa da kuma kwace Shari'ar Musulunci daga hannun matasa. Sun aiwatar da wannan shiri ne a cikin al’ummarsu domin kada matasan Kirista su shiga coci kuma suna aiwatar da wannan tsari a gare mu don kada matasan Musulmi su rika zuwa masallatai.


Ya ce game da ayyukan masu girman kan duniya a sararin samaniyar yanar gizo da ke adawa da akidar addinin musulmi: Yamma na neman bunkasa al'adu da salon rayuwarsu a cikin yanar gizo. Don haka, fasahar mu ita ce amfani da sararin samaniya a matsayin dandamali don yada tsantsar Islama na Muhammemadi da shigar da abubuwan da suka dace cikin gidajen yanar gizo, sararin samaniya, da hanyoyin sadarwar zamantakewa. Dangane da haka wajibi ne a samar da wani shiri na musamman ga matasa.

Babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya yi ishara da kokari da ayyukan Sheikh Ahmad Qomi a kasar Thailand ya kuma kara da cewa: Sheikh Ahmad Qomi ya kasance mai kira ne ga hadin kai da kusanci tsakanin musulmi kuma muna tunawa da shi sosai bayan shekaru 400 na mutuwarsa.

A karshe ya ce: Alhamdulillah yanayin musulmin Thailand yana da kyau; Yana da kyau a kula da wannan yanayi yadda ya kamata, kuma shugabannin musulmi su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

.........................