Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (A.S) ya ruwaito a safiyar ranar Juma’a ne Ayatullah Allama Sheikh Afif Al-Nabulsi ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya, kuma bayan shafe tsawon rayuwarsa yana mai bada ilmin da jihadi da kira zuwa ga Allah.
Kuma iyalan marigayi Ayatullah Sheikh Nabulsi sun yi jimamin wannan rashi ga Sahibuz Zaman (As) da kuma manya-manyan marajiai da makarantunsu, da kuma al'ummar masu gwagwarmaya da jihadi, wanda Shekh ya kasance abokin tafarkin shahidai biyu Sheikh Ragheb Harb da Sayyid Abbas al-Musawi, kuma wakilin Imam shahidi, Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr, Allah ya kara masa daukaka, kuma abokine ga boyayyen Sayyid Musa al-Sadr, Allah ya bayyanar da shi. Amincin Allah ya tabbata ga masanin fikihu kuma malami jarumi, Ayatullah Sheikh Afif Al-Nabulsi, wanda ya rasu a safiyar ranar Juma'a.
A cikin wata sanarwa da iyalan suka fitar sun ce: “Muna daga tafin hannunmu zuwa ga Allah domin mu yi masa addu’a da ya yalwata masa a gidajen Aljannar Firdausi, kuma Ya saukar da shi zuwa ga mafi kyawun matsayi, da abin da idanunsa suka tabbatar, kuma Ya karbe shi da shi mafi alherin karba, a gida mazauni da ba ya gushewa, da wurin na darajarsa da ba ta karkata, kuma shi ne mai ji kuma mai karbar addu'a."
An gudanar da jana'izar marigayi Ayatullah Sheikh Nabulsi tare da bunne shi a Majmau Sayyidah Zahra (AS) da ke kasar Sidon a ranar Juma'a da karfe shida na yamma, yayin da za a karbi ta'aziyyar maza da mata gabanin binnewa da bayan binnewa da kuma ranaku masu zuwa: Asabar da Lahadi, wato 15/16 ga watan Yuli, a cikin Majmauz Al-Zahra (a.s) daga karfe goma na safe zuwa sha biyu na rana da kuma karfe hudu na rana la'asar har bakwai da rabi na yamma.
Kungiyar malaman birnin Beirut, daya daga cikin ginshikan ilimi da tunani, ta yi jimamin rasuwar fikihim malamin mujahidan Ayatullah Sheikh Afif Al-Nabulsi, Mujahid kuma uba mai karfafawa ga gwagwarmaya da mayakanta, mai goyon bayan al'ummar Palastinu da gwagwarmaya tun kafuwar ƙungiyar a farkonta.
Cikin tsananin bakin ciki da wannan babban rashi, hukumar ta mika ta'aziyya ga malaman makarantun addini da Maraji'ai masu girma, da ma'abota tsayin daka, da dukkan muminai, tare da rokon Allah madaukakin sarki da ya yi rahama ga Marigayin masanin ilimi da hankali da jihadi ya kuma daukaka matsayinsa.
Muna mika ta'aziyyarmu da jaje ga huldar yada labarai a kungiyar Hizbullah.