1 Satumba 2022 - 20:14
Isra’ila Ta Sake Kai Wa Filin Jirgin Saman Aleppo Hari

Isra’ila ta sake kai wa filin jirgin saman Aleppo wani harin sama, inda bayanai ke cewa an samu barna.

Kamfanin dilancin labaren Siriya na Sana, ya rawaito cewa wasu makamai masu linzami 4 da jiragen Isra'ila suka harba daga tekun Mediterrenean kusa da birnin Latakia da ke gabar teku sun afkawa filin jirgin saman Aleppo da yammacin ranar Laraba.

Baya ga hakan a cewar Sana, makamman garkuwa game da hare haren sama na Siriya, sun murkushe hare haren, inda suka kakkabo makamai da dama, amma wasu sun afka cikin yankin Kiswa.

A nata bangare kungiyar kare hakkin bil adama ta Syria OSDH dake cibiya a Biritaniya, ta ce an kai harin ne kan titin jirgin sama, inda gobara ta tashi.

Wannan dai shi ne karo na 23 da Isra'ila ke kai hare-hare kan wasu yankuna a Siriya tun farkon wannan shekara, a cewar kungiyar kare hakkin bil'adama ta Siriya.

A ranar 25 ga watan Agusta, jerin hare-haren "daga cikin mafi muni" da Isra'ila ta kai kan sansanin soji a kusa da Hama a tsakiya da kuma Tartous a yamma sun yi sanadin mutuwar mutane da jikkata.

A farkon watan Yuni, wasu munanen hare-hare da Isra’ilar ta kai sun sa titin jirgin sama daya tilo da ke aiki a filin jirgin saman Damascus ya daina aiki na tsawon kwanaki da yawa.

342/