24 Agusta 2022 - 19:09
Kasar Turkiya Ta yi Alkawarin CI Gaba Da Goyon Bayan Falasdinawa

Shugaban kasar Turkiya Dayyib Rajab Erdogan ya sanar da cewa kasarsa ta yi Alkawarin ci gaba da nuna goyon bayanta ga alummar Falasdinu , yana mai kare cewa kyautata dangantakar alaka da ta yi da Israila ba zai shafi dangantakar dake tsakaninsu ba

A makon jiya ne kasar Turkiya ta mayar da alakar diplomasiya da Isra’ila bayan mataki na karshe da bangarorin biyu suka dauka na sasanta tsakaninsu

Shugaban na Turkiya yayi wannan bayani ne a lokacin ziyarar da shugaban gwamnatin kwarya kwaryan cin gashin kai mahamud Abbas Abu mazin ya kai turkiya mako guda bayan turkiya da isra’ila sun sanar da yanke shawarar dawo da dangantakar Diplomasiya da musayar jakadu tsakaninsu a karon farko tun bayan da dagantakar ta tabarbare a shekara ta 2018

Anasa bangaren mahamud Abbas ya jinjinawa kasar turkiya game da irin goyon bayan da take bawa alummar falasdinu sai dai bai ce komai ba game da mayar da alaka da ta yi da isra’ila , yace muna sane da irin goyon bayan da take bawa falasdinawa wajen kare hakkokinsu da fafutukar kafa kasa mai yanci da suke yi

342/