Wannan na zuwa ne bayan samun sama da mutane 100 da aka tabbatar ko ake zargin sun kamu da cutar a Turai a baya-bayan nan.
A wani abu da Jamus ta kira barkewa mafi girma a Turai, an tabbatar da samun wadanda suka kamu da cutar a akalla kasashe 5 da suka hada da Biritaniya da Spain da Portugal da Jamus da Italiya, har ma da Amurka da Canada da Australia.
Cutar wadda aka fara gano ta a tsakanin birrai dake yaduwa ta hanyar mu’amala, ba kasafai ake samunta a wajen nahiyar Afrika ba, don haka, batun ya zama abun damuwa.
Sai dai, masana kimiyya ba sa tsammanin barkewar cutar za ta zama annobar duniya kamar COVID-19, bisa la’akari da cewa, kwayar cutar ba ta da saukin yaduwa kamar ta COVID-19.
342/