18 Mayu 2022 - 19:24
Lebanon: An Bada Sanarwan Cikekken Sakamakon Zabe Na Majalisar Dokoki A Lebanon

Sakamakon zaben majalisar dokoki a kasar Lebanon wanda aka gudanar a ranar lahadi 15 ga watan Mayu da muke ciki ya nuna cewa yanzun kuma ba kawancen Hizbulla ne ke da rinjaye a majalisar ba, don kawancen ya sami kujeru 58 kasa da 65 da ake bukata na samun rinjaye a majalisar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sannan jam’iyya ,afi karfi a “tayyar al-watan al- hur ba ita ce jam’iyya mafi karfi a majalisar dokokin kasar ba, don tana da kujeru 18, a yayinda jam’iyyar “Sojojin Libnon” wacce take hamayya da ita take da kujeru 20.

Banda haka an sami kujeru 16 kari a majalisar na wadanda suka shigo zaben ba karkashin wata jam’iyya ba.

Sannan a karon farko cikin shekaru masu yawa an gudanar da zaben majalisar dokokin kasar ta Lebanon ba tare da jam’iyyar Mustakabal da sunna ba.

Wasu sun amince da matsayin da shugaban jam’iyyar Saadul Hariri ya dauka na kauracewa zaben, sannan wasu kuma sun fice daga jam’iyyar don shiga takara karkashin wasu jam’iyyun.

Sai dai Jubran Basil na tayyar watan alhur ya ce har yanzun kawancensu ne take da rinjaye a Majalisar, kuma suna da damar aiwatar da al-amura na ci gaban kasa da diyaucin kasar fiye da da.

342/