6 Mayu 2022 - 19:03
Wasu Da Ba’asan Ko su Waye Ba Sun Kashe Yahudawa 3 A Kusa Da Birnin TelAviv

Jami’an yan sandan Isra’ila sun bayyana cewa akalla yahudawa guda 3 ne suka halaka yayin da wasu guda 4 uma suka jikkata sakamakon hari da wasu masu dauke da makami da ba’a san ko suwa ye ba suka kai mu a kusan da birnin Tel aviv. Halin wasu daga cikinsu rai kwakwai mutu kwakwai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yan sandan sun kaddamar da samame loko-loko don gano wadanda suke aikta kisan, inda suka kafa shingaye bincike da kuma amfani da jirgin saman mai saukar Ungulu domin bincike ta sama.

Wannan hari yanzu ne a daidai lokacin da isra’ila take bukin zagayowar ranar kafuwarta , inda tuni suka fara kai hare hare kan falasdinwa da ynakunansu da suka mamaye

Kungiyar Hamas ta jinjinawa wadanda suka kai harin na Elad tare da bayyana shi a matsayin na jarumta , kuma wani martani game da ci gaba da kai hare-hare da sojojin Isra’ila suke yi musamman a masallacin kudus mai tsarki.

342/