30 Afirilu 2022 - 19:20
​An Raya Ranar Kudus Ta Tuniya A Fiye Da Kasashe 90 A Duniya

An raya ranar kudus ta duniya a kasashe kimani 90 a diniya a jiya Jumma 29 ga watan Afrilu, wanda yayi dai dai da ranar 27 ga watan Ramadan na wannan shekara ta 1443H.K.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafafen yada labarai da damaa duniya sun bada labarin raya ranar kudus ta duniya, tare da fito zanga-zanga kan tituna da kuma gudanar da tarurruka don wayar da kan mutane danga da matsalolin al-ummar Falasdidu wadanda suka kara tabarbarewa a ko wacce rana.

Al-ummu da kasashen da suke goyon bayan al-ummar Falasdinu suna kara yawa a ko wace shekara.

A nan Iran an gudanar da jerin gwano na yin allwadai da haramtacciyar kasar Isra’ila a garuruwa da dama, bayan da a cikin shekaru 2 da suka gabata saboda cutar Korona an gudanar da su ne a cikin motoci.

342/