28 Afirilu 2022 - 22:04
Iran: Jagora Zai Gabatar Da Jawabin Ranar Quds Kai Tsaye A Gobe Juma'a

Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei zai gabatar da jawabi kai tsaye a gobe Juma'a kan ranar Quds ta duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafofin yada labarai na cikin gida za su watsa jawabin kai tsaye wanda zai gabatar da misalin karfe 4 a gogon Tehran a yammacin gobe Juma'a. kamar kowace shekara dai jagoran juyin juya halin muslucni ya kan gabatar da jawabi kai tsaye a duk ranar Quds ta duniya, inda ya kan yi jawabin nasa a cikin harsunan Farisanci da larabaci. A gobe juma'ar karshe ta watan Ramadan za agudanar da taruka da gangami na ranar Quds ta duniya a kasashen duniya daban-daban, domin nuna goyon baya ga al'ummar falastinu, da kuma yin Allawadai da zaluncin Isra'ila, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da take yi.

342/