Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Muhammad Ra’ad wanda ya gabatar da jawabi ta hanyar bidiyo daga nesa ga taron da aka shirya a birnin San’aa na kasar Yemen mai taken: “ Palasdinu A Matsayin Babban Batun Dake Gaban Al’umma”,inda ya kara da cewa; Idan abokin gaba ya yi karo da karfin da muke da shi, to zai rushe a gaban jajurcewarmu.”
Muhammad Ra’ad ya kuma jaddada muhimmacin hadin kan al’umma domin ‘yanto da Palasdinu, domin idan ba haka ba, za a sami koma baya.”
Bugu da kari, shugaban wakilan gwagwarmaya a majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya ce; Kulla yarjejeniyar da wasu kasashen wannan yankin suke yi da makiya, ko kadan ba zai amfani al’ummarmu ba.”
Taron na kasar Yemen dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya a ranar jumar karshe ta watan Ramadan mai zuwa.
342/