24 Afirilu 2022 - 16:51
Shugaban Iran: Kasashen Turai Ne Ummul-Haba’isin Ta’addancin Da’ish Da HKI

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isy ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa; Zaluncin da ‘Yan Sahayoniya suke yi wa masallata Palasdinawa a masallacin kudus, da laifukan da kungiyar Da’ish ta tafka akan mutanen da suke ciki halin salla a wani masallaci na kasar Afghanistan, kirkira ce ta kasashen turai da ‘yan sahayoniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban kasar na Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahadar Imam Ali ( A.S ), ya yi bayani akan cewa “sunnar Ubangiji ce ya taimakawa mutane masu rauni da wadanda ake zalunta.”

Shugaban kasar ta Iran Sayyid Ra’isy ya kuma ce; Shirin da aka yi na cewa za a warware matsalar palasdinu ne ta hanyar tattaunawa akan teburi ya ci tura, don haka abinda yake faruwa a yanzu shi ne Masu jihadi ne za su ayyana makomar Palasdinu.

Dangane da ranar Kudus ta duniya wacce ake yi a juma’ar karshe ta watan Ramadan, shugaban kasar ta Iran ya ce; Wannan rana ce ta hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi domin birnin Kudus da masallacinsa.

342/