21 Afirilu 2022 - 20:38
Iran Ta Kaddamar Da Sabon Jirgin Yaki Maras Matuki Da Ta Kera Samfurin Kaman-22

Ma'aikatar tsaron kasar Iran ta kaddamar da sabon jirgin yaki maras matuki da injinoyin kasar suka kera samfurin kaman-22.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan sabon jirgin yaki maras matuki dai ya sha banban da sauran wadanda Iran ta kera, ta fuskar irin ayyukan da yake yi, da suka hada da tafiya ta tazara mai nisan gaske na dubban kilo mitoci, sanann kuma yana kai hari da makamai masu linzami da yake dauke da su. baya ga haka kuma a lokaci guda yana gudanar da ayyuka na tattara bayanan sirri na makiya tare da aiko su kai tsaye zuwa wurare na musamman da aka tanada domin samun bayanai daga gare shi. Sanan kuma ya kan yi tashi zuwa tazara mai nisa a cikin sararin samaniya, ta yadda ya bace wa na'urorin rada na makiya.

342/