Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin yada labarai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce, Amir Abdollahian ya bayyana a cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho da aka yi a yammacin jiya Laraba, matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da yaki, da kuma wajabcin mai da hankali kan hanyar da za a warware shi hanyar siyasa, tattaunawa ta diflomasiya.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da a shirin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na aikewa da tawagar likitoci daga kungiyar agaji ta Red Crescent zuwa kasar Ukraine, inda ya kara da cewa: Wajibi ne a samar da cikakken tsaro ga wuraren diflomasiyya, domin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Kyiv shi ne zai karbi tawagar loitocin.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Ukraine ya taya murnar zagayowar watan Ramadan mai alfarma tare da godewa tare da jinjinawa matsayin Iran bisa nuna rashin amincewa da yakin, sannan ya ce gwamnatin Ukraine za ta yi iya kokarinta na kiyaye wuraren diflomasiyya.
Kulba ya kuma tabbatar da matsayin kasarsa na neman dakatar da yaki da rikici, ya kuma yi maraba da ci gaba da tattaunawa da takwaransa na Iran, yana mai bayyana fatansa na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a bangarori da matakai daban-daban.
342/