A jawabin da ya yi yayin taron majalisar ministocinsa na karshe, firaministan na Ivory Coast mai murabus, Patrick Achi, yace shugaba Ouatara ya amince da murabus din gwamnatin kuma zai nada sabon firaministan mako mai zuwa da zai gabatar masa da sabbin mambobin gwamnati.
Domin cika alkawuran da gwamnati ta dauka da kuma tunkarar tabarbarewar tattalin arziki a duniya da ake fama da shi yanzu, na dauki matakin rage yawan ministoci na gwamnati a cewar shugaba Ouatara.
Ya kara da cewa ya zama dole a rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, a kuma karkata su wajen gudanar da ayyukan al’umma da kuma wadanda suka shafi harkar tsaro.
342/