Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shehbaz Sharif, mai shekara 70, jagoran jam’iyyar islama ta PML-N a Pakistan, na daga cikin jam’iyyun adawa na kasar da suka kai ruwa-rana na ganin an tsige Imran Khan, wanda ‘Yan jam’iyyarsa ta PTI, ke zargin Amurka da kitsa tsige shi.
Shehbaz Sharif, wanda aka bayyana da gogaggen dan siyasa, ya kwashe shekaru a matsayin gwamnan yankin Pendjab, sannan kuma kani ne ga babban dan siyasan nan na Pakistan Nawaz Sharif, wanda ya rike mukamin firaminista har sau uku a kasar.
Ya kuma jima da yake gudun hijira a Biritaniya, bayan zarginsa da cin hanci da rashawa.
Yanzu Shehbaz Sharif, zai kafa gwamnati ta kawance tare da sauren jam’iyyun adawa, saidai babbar ayar tambayar da ake azawa it ace ko sabuwar gwamnatin za iya kai labari kafin zaben ‘yan majalisar dokoki da za’ayi nan da shekara guda a daidai lokacin da kasar ke fama da matsanancin matsin tattalin arziki da kuma zanga zangar da ta kunno kai ta magoya bayan firaministan da aka tsige Imran Khan.
342/