10 Afirilu 2022 - 20:40
Wata Balasdiniya Ta yi Shahada Sakamakon Bude Mata Wuta Da Sojojin Isra’ila Suka Yi

Sojojin Isra’ila sun harbe wata bafalasdiniya a kuda da garin Baith laham dake kudancin gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, adaidai lokacin da rikici ke kara yaduwa a yankunan falasdinawa da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar cewa sojojin Isra’la sun bude wuta kan wata mata mai suna Ghada Ibrahim alokcin da take kokarin ketara wurin binciken ababen hawa na soji a kusa da kauyen Husan wake yammacin baithlaham

Matar yar shekaru 40 da haihuwa ta mutu ne a Asibiti a bait jala dake gabar yammacin kogin Jodan inda aka kaita domin yimata magani bayan da tayi ta zubar da jinni sakamakon harbin da aka yi mata

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila suka kara tsaurara mataken tsaro a yankunan falasdinawa bayan harin da wani bafalasdine ya kai a birnin tel Aviv a baya bayan anan da yayi sanadiyar halakar yahudawa 2 da kuma jikkata wasu 15.

342/