8 Afirilu 2022 - 20:24
Kungiyar Ansarulla Ta Yamen Ta yi Maraba Da Murabus Da Mansur Hadi Yayi Daga Kan Mukaminsa

Shugaban kasar Yamen dake gudun hijira wanda ke samun goyon bayan kasar Saudiya ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa, kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta yan Huthi ta bayyana matakin da cewa ya zai tana majalisar dinkin duniya Uzurin ci gaba da goyon bayan yakin da kasar Saudiya ke jagoranta a kasar na tsawon shekaru bakawai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Acikin wani bayani da mai Magana da yawun kungiyar Ansarullah shugaban ya wallafa a shafinsa na Twiter mohammad Abdussalam yace gwamnatin Abdu Rabbuh Mansur Hadi ta zo karshe wanna ci gaban da aka samu ya karyata kasahen da suka fake da kai wa kasar Hari da sunan murkushe masu yunkurin juyin mulki a kasar

Yace yanzu manyan hukumomin na duniya ba su da sauran Uzuri na ci gaba da amfani da Kalmar kare halatacciyar gwamnatin yamen wajen ci gaba da yin kisan kiyashi kan alummar Yamen da kuma ci gaba da killace iyakokin ruwa da sama na kasar

Daga karshe ya soka game da tattaunawar da aka yi da kasar saudiya ta karbi bakunci na warware rikicin kasar Yamen y ace Alummar yamen ne suka fi cancanta su fayyace makomar kasarsu ba wasu daga waje ba.

Tuni dai kungiyar Ansarullah ta kauracewa zaman na Riyadh da kungiyar kasahen yankin tekun fasha ta jagoranta day a kunshi wakilin gwamnatin hadi Mansur da saudiya ke goyon baya da kuma manzon musaman na Amurka kan kasar yamen Tim Linderking.

342/