Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An yi gangamin ne a cikin birnin Khartum da kuma wasu birane daban na kasar ta Sudan da su ka hada a Um-Durman, Port-Sudan da Qadarif, suna kuma masu yin tir da juyin mulkin da sojojin kasar su ka yi a watan Oktoba na shekarar da ta gabata.
A watan Aprilu na 2019 ne dai sojoji su ka kifar da gwamnatin Umar Hassan al-Bashir bayan da al’ummar kasar su ka dauki watanni suna gunadar da Zanga-zangar kin jinin shugaban saboda tashin farashin kayan masarufi.
Al’ummar ta Sudan suna ci gaba da gudanar da Zanga-zanga domin nuna kin amincewa da juyin mulkin da sojoji su ka sake yi a 2021.
342/