4 Afirilu 2022 - 19:24
Iran A Shirye Take Ta Taimaka Wa Qatar Domin Gudanar Da Wasannin Kwallon Kafa Na Duniya Cikin Nasara

Shugaban Kasar Iran Hujjatul-Islam Ibrahim Ra’isi wanda ya yi Magana ta wayar tarho da sarkin katar Tamim Bin Hamad ali-Thani cewa; Ci gaba da bunkasa alaka a tsakanin kasashensu zai taimawa al’ummunsu ne, kuma zai taimaka wajen shimfida zaman lafiya da tsaro a cikin wannan yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dangane da ziyarar da sarkin na Qatar zai kawo nan Iran nan gaba kadan, shugaban kasar ta Iran din ya ce; A yayin wannan ziyarar kasashen biyu za su sake daukar matakai a fagegen ayyuka a tsakaninsu.

Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce; Dukkanin kasashen biyu suna da azama mai karfi ta ci gaba da fadada alakar tasu.

Tun da farko dai, shugaban kasar na Iran ya taya sarkin Qatar din murnar shigowar watan azumin Ramadan mai alfarma, sannan kuma ya tabbatar da cewa; Iran a shirye take ta taimaki kasar tasa domin ganin ta gudanar da wasannin karshe na gasar cin kofin duniya na kwallon kafa cikin nasara.

342/