19 Oktoba 2026 - 11:50
Source: ABNA24
Iran: Muna Ƙididdigar Lokaci Don Maida Martini Ga Shirye-Shiryen Wauta Na Maƙiyi

Shugaban Babban Hafsoshin Sojoji kuma babban Kwamandan Sansanin Khatam al-Anbiya, yayin da yake nuni ga ƙudurin jagoranci, al'umma, jami'ai, da sojojin Iran na Musulunci masu ƙarfi, ya yi wa maƙiya gargadi: "Ƙarar hari na gaba zai fi kusa, yafi haifar da barna, kuma ba za a iya kakkabo shi ko dakatar da shi ba."

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Shugaban Babban Hafsoshin Sojoji kuma Kwamandan Sansanin Khatam al-Anbiya, yayin da yake jawabi ga shugabannin maƙiyin Amurka da sahyoniya, ya ce: "Waɗannan taken da kuke faɗi, da kun isa da kun iya aiwatar da su zuwa yanzu. A kowane yaƙin da ya gabata, kun shiga yaƙi da taken kifar da Jamhuriyar Musulunci, raba Iran, da lalata ta; yayin da a yau kuke cikin halaka da kifarwa ku, kuma Iran mai ƙarfi tana nan kafe."

Babban Janar Abdollahi ya kara da cewa: "Shugaban Amurka ya tsufa kuma ba ya da ikon tashi daga wurin da yak e zaune, al'ummar Amurka da mazauna yankunan da aka mamaye sun sani da kyau cewa kuna da matsaloli masu tsanani na tushe, kuma dole ne su sani cewa kuskuren lissafinku na gaba zai haifar da martani daban-daban da suka fi tsanani fiye da da."

Shugaban Babban Hafsoshin Sojoji kuma Kwamandan Sansanin na Khatam al-Anbiya, yayin da yake nuni ga ƙudurin jagoranci, al'umma, jami'ai, da sojojin Iran na Musulunci masu ƙarfi, ya yi wa maƙiyi gargadi da cewa: "Kun sha gwada wannan ƙuduri da niyya sau da yawa, kuma sake gwada abin da aka riga aka gwada kuskure ne; muna kididdigar lokacin shirye-shiryenku na wauta domin mayar da martani. Ƙarar hari na gaba zai fi kusa, yafi haifar da barna, kuma ba za a iya kakkabo shi ko dakatar da shi ba."

…………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha