Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan matakin na zuwa ne bayan da firaministan kasar Imran Khan, ya bukaci hakan ga shugaba Alvi, jim kadan bayan soke wani yunkurin tsige shi da aka gabatarwa majalisar.
Rusa majalisar zai bada damar kiran zaben ‘yan majalisar dokoki na kafin karshen wa’adi a cikin kwanaki casa’in masu zuwa.
A wani labarin kuma Ministan yada labarai na Pakistan din, ya sanar da cewa firaministan kasar ya mika takardar murabus din gwamnatinsa amma zai ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnatin har zuwa lokacin zabe kamar yadda dokokin kasar suka tanada.
‘Yan adawan Pakistan dai na dora alhakin tabarbarewar tattalin arzikin kasar ga firaministan da kuma gazawa a siyasar ketare, lamarin da ya sa suka gabatar da batun neman tsige shi, saidai tun kafin zaben majalisar ta yi watsi da batun.
342/