2 Afirilu 2022 - 11:17
Al’ummar Palasdinawa Sun Yi Tarukan Raya Ranar Kasar

An gudanar da taruka da jerin gwano a yankuna mabanbanta na Palasdinu domin tunawa da ranar kasa da ake yi a kowace shekara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yankunan da aka yi gangami da jerin gwanon sun hada Gaza da yammacin kogin Jordan.

Shekaru 46 da su ka gabata a 1976 ne dai al’ummar palasdinu su ka gabatar da bore domin nuna kin amincewarsu da kwace kasa da ‘yan sahayoniya suke yi daga palasdinawa da zaunar da yahudawa a ciki.

Sai dai ‘yan sahayoniya sun yi amfani da karfi akan al’ummar palasdinu domin murkushe boren nasu, inda su ka kashe da dama daga cikinsu da kuma kama wasu da suka 300.

A shekarar bana ranar kasar ta zo ne a lokacin da Palasdinawan suke kai hare-hare akan ‘yan mamaya. A cikin makon da ya shude palasdinawan sun kashe ‘yan mamaya shida a lokuta da dama.

Yahudawan Sahayoniya sun kwace fiye da 60% na kasar yammacin Kogin Jordan,yayin da aka barwa Palasdinawa kaso 15% domin kafa gwamnatin jeka nayika.

Adadin Palsdinawan da ‘yan sahayoniya su ka tilastawa hijiyi daga birnin Kudus sun kai 14500. A halin yanzu da akwai ‘yan share wuri zauna 700,000 da suke rayuwa akan kasar Palasdinawa da aka kwace. Da akwai matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna 503 da suka hada wasu 29 a birnin Kudus.

342/