30 Maris 2022 - 14:41
Rasha Da Ukraine Sun Fara Tattaunawar Gaba Da Gaba A Turkiyya

Wakilan kasashen Rasha da Ukraine sun fara tattaunawar gaba da gaba a birnin Santambul na Turkiyya, a daidai lokacin da rikicin kasashen biyu ya shiga kwana na 33.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yayin wani jawabi lokacinda da yake karbar tawagogin wakilan kasashen biyu Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, ya bukaci bangarorin biyu su yi amfani da wannan dama domin kawo karshen zubar da jini.

‘’ Duniya gaba daya na jiran jin sako mai dadi daga gare ku’’ inji mista Erdogan.

Shugaban na Turkiyya ya kuma goyi bayan dukkan bangarorin biyu kan bukatunsu wanda ya danganta da halattatu.

342/