25 Maris 2022 - 21:20
​Iran Tana Tattaunawa Da Rasha Kan Shiga Tsarin Musayar Kudade Ta MIR

Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana cikin tattaunawa da gwamnatin Rasha dangane da shigarta cikin tsarin musayar kudade tsakanin bankuna da ciboyoyin kasuwanci wanda ake kira MIR.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Jalali jakadan kasar Iran a Mosco yana fadar haka.

Kasar Rasha dai ta fara amfani da wannan tsarin tun ranar daya ga watan Mayun shekara ta 2017. Babban bankin kasar Rasha ne ya samar da wannan tsarin musayar kudade wanda yake kama da na SWIF wanda kasashen yamma suke iko da shi.

Kasashen Iran da Rasha dai suna fama da takunkuman tattalin arziki na kasashen yamma daga cikin har da musayar kudaden tsakanin bankuna wanda ake kira Swif, shiga kasar Iran wannan tsarin zai taimaka mata wajen sawwaka takunkuman na kasashen yamma.

Kasar Rasha dai ta bukaci kasashen da suka dora mata takunkuman tattalin arziki da rika biyan kudaden makamashi da duk abinda zasu saya daga kasar Rasha da kudaden kasar. Kasashen turai suna sayan kasha 40% na makashin da suke bukata daga kasar Rasha.

Kuma kasashen sun hada da Amurka, kasashen kungiyar EU, Canada, Burtanioya, Japan, Norway da kuma Singapore.

342/