20 Maris 2022 - 22:12
Yakin Rasha Da Ukraine Ya Shiga Kwana Na 25

Sojojin Rasha na ci gaba da kokarin yi wa Kiev babban birnin kasar Ukraine kawanya, yayin da aka shiga kwana na 25 na Rasha da Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A halin da ake ciki dai mutum miliyan goma ne suka kauracewa muhallensu tun bayan kutsen sojin Rashar a Ukraine, inji majalisar Dinkin Duniya.

A cewar shugaban hukumar koli mai kula ‘yan gudun hijira ta MDD, Filippo Grandi, a cikin ‘yan gudun hijirar sama da miliyan uku sun riga sun fice daga Ukraine.

Haka zalika kuma kimanin mutum 847 ne suka mutu tun farkon yakin, sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai 1399.

342/