Da yake bayyana hakan ga manema labarai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzadeh ya ce bayan doguwar tattaunawa, gwamnatin Burtaniya ta biya Iran bashin da take binta bayan tsaikon sama da shekaru 40.
Khatibzadeh ya ce hukumar shari'a ta Iran ta yanke shawarar sakin 'yan Birtaniyya ‘yan asalin Iran din wadanda suka yi wani bangare na hukuncin da aka yanke musu bisa dalilai na tausayawar addinin musulinci da kuma jin kai, Wanda kuma bai da wata alaka tsakanin biyan bashin da sakin fursunonin.
Sannan ya yabawa kasar Oman akan shiga tsakanin da ta yi kan wannan batu.
A jiya ne Iran, ta sallami ‘yan biritaniyar biyu Nazanin Zaghari-Ratcliffe da Anoosheh Ashoori wanda tuni suka koma biritaniya bayan shakara shida a tsare gidan yari.
342/