Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan wata alama ce ta kawo karshen sabanin dake akwai game da yunkurin da ake na farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Ministan harkokin wajen Rasha ne Sergueï Lavrov, ya bayyana hakan, inda ya ce sun samu garanti a rubuce kuma an sanya su a daftarin neman ceto yarjejeniyar nukiliyar ta Iran.
Mista Lavrov, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da takwaransa na Iran, Hossein Amir-Abdollahian ya kai a birnin Moscow ranar Talata.
A karshen makon da ya gabata ne aka dakatar da tattaunawar da ake a Vienna da nufin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran, saboda bukatun na Rasha.
342/