Majiyar mortar jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto KhadibZadeh yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron daliban jami’a da malamansu Iraniyawa wadanda suke karatu a kasashen waje, wanda aka gudanar a birnin Mashad na arewacin kasar. Wannan dai shi ne taro karo na 15 wanda daliman da malamansu suke shiryawa a ko wace shekara.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kara da cewa kasar Iran bata goyon bayan ko wani bangaren a yakin da ke faruwa a kasar Ukrain, amma kuma Iran ta san cewa fiye da shekaru 30 da suka gabata kungiyar tsaro ta NATO tana shiryawa wannan yakin, saboda fadada kungiyar tsaro ta NATO da take yi a gabancin Turai.
Daga karshe ya bayyana cewa kasar Iran a cikin wannan halin da ake ciki a duniya tana cike da karfinta da kuma ci gaba da nuna turjiya kan kasashen da suke kiyayya da ita.
342/