Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tun da farko dai yi tsamannin a makon jiya za’a cimma matsaya a tattaunawar da aka shafe dogon lokaci anayi tsakanin wakilan Iran da na manyan kasashen duniya.
Shugaban kula da manufofin ketare na kungiyar tarayyar turai, Josep Borrell, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa an dan dakatar da tattaunawar saboda wani sabani da ya bullo.
Ya kara da cewa an kammalla komi, kuma daftarin na kan tebur tsaf.
Bayanai dai sun ce Rasha dai na mai son a bata tabbacin cewa takunkuman da kasashen turai da Amurka suka kakaba mata ba zasu shafi alakar kasuwancinta da Iran ba.
Wata majiya a kungiyar tarayyar turai ta bayyana cewa, yanzu ya rage ga Iran da China dasu tattauna domin shayo kan lamarin.
Saidai kuma wani jami’in diflomatsiyyar EU, ya ce idan ba’a shayo kan Rasha ba, akwai wasu damamaki da ake dasu.
342/