8 Maris 2022 - 15:51
Isra’ila Tana Shirin Rusa Gidan Wani Fursinan Siyasa A Yammacin Jenin

Wata majiyar radiyon yahudawan Isra’ila ‘yan mamaya bada sanarwan cewa gwamnatin HKI tana shirin rusa gidan falasdinawa 2 Umar da Ghaith Jarradat dake kudancin birnin Jenin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Labarin ya kara da cewa a jiya ma sojojin yahudawan sun nufi unguwar Silatul-Harithiyya da ke yamma da garin Janin, amma mayakan saraya Qus sun tilasta masu komawa baya. Sojojin HKI sun kama Ghaith da shakikinsa Umar ‘yan shekara 21 a duniya ne da kawunsu sheikh Muhammad Yusuf Jarradat a wani sumame da suka kaiwa yankinsu silsilatul Harithiyya kimani watan guda kenan, tare da zargin suna da hannu a wani harin da mayakan sara quds sukakaimasu

342/