6 Maris 2022 - 19:48
Saudiyya Ta Dage Takunkumin hana Yin Umrah Da ta Sanyawa Wasu kasashe Ciki Har da Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa Mahukunta a kasar Saudiyya sun cire takunkumin da ya hana ‘Yan Najeriya shiga kasar saboda Covid19.

Daga cikin kasashen da janye takunkumin na kasar ta Saudiyya ya shafa, sun hada da Kasar Namibia da Afirka ta Kudu sai Afghanistan da Botswana da Zimbabwe da Lesotho da Eswatini da Mozambique da Malawi da Mauritius da Zambia da Madagascar.

Sanarwa ta fita a shafin hukumomin kasar da ke kula da Masallatai biyu masu alfarma na Makkah da Madina. Yanzu ‘Yan Nijeriya za su iya ci gaba da zuwa umara bayan janye takunkumin hana shiga kasar da Saudiyyan ta yi a kwanakin baya.

342/