4 Maris 2022 - 20:32
Sudan Ta yi Marhabin Da Yarjajeniyar Da Ta Kulla Da Rasha Ta Kafa Sansanin Soji A Kogin Bahar Maliya

Mataimakin shugaban majalisar mulki na kasar Sudan Janar Mohammad Hamdan ya fadi cewa ya tattaunawa da jami’an kasar Rasha kan harkokin da suka shafi tsaro, Da yake taron manema labarai a filin saukar jiragen sama dake Birnin Khartum bayan kammala ziyarar kwanaki 8 a kasar Rasha ya bayyana cewa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - daga cikin tattaunawar da ta gudanar tsakaninsa da jami’an gamnati kasar ta Rasha, sun tattauna kana irin hanyyoyi da kasashen biyu za su yi aiki tare da kuma sauran batutuwan da suka shafi tsaron kasa. siyasa Tatatalin arzki kuma ziyar tayi armashi sosai

Har ila yau ya face cewa a ganawarsa da shugaban majalsiar tsaron kasar rasha Nikolay Patrushev sun tattauna kan batun tsaron a rasha da sudan da kuma bangarorin da bangarorin biyu za su iya yin aiki tare , da suka gada da Fada da Ta’adanci sa kuma bunkasa Ilimi.

Daga karshe ya nuna cewa game da batun abin da ya shafi sojojin ruwa kuwa kasar Rasha za ta kafa sansanin sojin ruwa a tashar jirgin ruwan kasar Sudan a tekun Baharmaliya.

342/