Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto babban sakataren majalisr koli da tsaron kasar Ali Shamkhani yana fadar haka a safiyar yau Laraba a gaban wasu yan majalisar dokokin kasar a nan birnin Tehran.
Labarin ya kara da cewa shamkhani ya je majalisar dokokin kasar Iran ne don sanar da yan majalisar Irin halin da ake ciki dangane da tattaunawar dagewa Iran takunkumai a birnin Vienna na kasar AUtria da kuma shirye-shiryen gwamnatin shugaba Ibrahim Raesi dangane da tattalin arzikin kasar.
A lokacin ganawar dai Shamkhani ya fadawa ‘yan majalisar abubuwa masu muhimmanci wadanda har yanzun ana tattaunawa a kansu a taron na Vienna.
Daga karshe yan majalisar sun yabawa tawagar tattaunawan kasar a Vienna da kuma nuna cewa kasar Iran ta tsallawa lokaci mafi hatsari da ke tattare da takunkuman wadanda suke takurawa mutanen kasar.
342/