27 Faburairu 2022 - 15:05
Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Wani Makami Mai Linzami

Rahotanni daga koriya ta Kudu, na cewa makobciyar kasar koriya ta Arewa ta harba wani makamai mai linzami a wannan Lahadin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rundinar sojin koriya ta Kudu ta ce an harba makamin ne zuwa tekun Japan.

Harbin shi ne irinsa na farko cikin wata guda, amma kuma na takwas a bana.

Fadar shugaban koriya ta Kudu, ta nuna matukar damuwarta kan harbin, wanda ta ce ya zo ne a daidai lokacin da duniya ke kokarin shawo kan yaki a Ukraine.

342/