ABNA24 – Majiyar labaran kasar Labanon ta bayyana cewa a daren jiya ma jiragen yakin HKI sun yi shawagi a sararin samaniyar garin Tyre na tsawon lokaci kana kuma ya sauko kasa- kasa a sararin samaniyar birnin Berut da hakan keta kudurin majalisar dinkin duniya ne,
Ana sa bangaren shugaban kasar Labanon Michel Aoun yayi tir da wannan matakin na Isra’la na wuce gona da iri, yace barazanar da suke fuskanta daga Israila shi ne babban abin ya damu gwamnatin kasar Labanon.
Ministan harkokin wajen kasar Labanon ya dade yana kai koke gaban majalisar dinkin duniya da ma kwamitin tsaro game da keta hurumin sararin samaniyar Kasar da Isra’ila ke yi ba dare ba rana.
Wannan yana zuwa ne bayan da kungiyar Hizbullah ta aike da jirgin sama mara matuki a yankin falasdinu inda ya kammala shawagi ya je ya dawo ba tare da Isra’ila ta Ankara ba.
342/