ABNA24 – wani makami mai linzami da aka harbo daga yankin ‘ yan awaren ya fadi a daidai lokacin da ministan harkokin cikin gidan Ukiraniya yake ziyarar aiki a filin daga.
Majiyar ta kara da cewa; Tuni an dauke jami’an gwamnati da kuma ‘ yan jarida da suke a yankin, domin kare lafiyarsu.
A wani gefen masu tafiyar da sha’anin mulki a yankin na Donbass sun sanar da cewa sun dauke farafen hula 13,000 daga yankin zuwa cikin kasar Rasha domin basu kariya.
A can cikin kasar ta Rasha, mahukunta a yankunan da suke kan iyaka da Ukiraniya sun sanar da kafa dokar ko-ta-kwana domin karbar masu kwararowa daga cikin yankin da ake fadan.
Bangarorin gwamnatin Ukiraniya da ‘yan aware sun yi musayar zargi akan wanda ya fara bude wuta.
Ana zaman dar-dar a kan iyakokin Rasha da Ukiraniya saboda tsoron barkewar yaki.
342/