15 Faburairu 2022 - 16:38
​Shamkhani: Rashin Cika Alkawulan Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duk Wata Yarjejeniya Da Amurka

Shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewa rashin cika alkawula, ita ce babbar barazana ga dukkan yarjeniyoyin da za’a kulla kan shirin nukliyar kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya nakalto Ali Shamkhani yana fadar haka a shafinsa na twitter a yau Talata. Ya kuma kara da cewa dagewa iran takunkuman tattalin arziki shi ne ya zaman Iran tana iya dogaro da kanta a dukkan bangarorin tattalin arziki da take da su.

Jami’an ya kara da cewa duk wata yarjejeniya da Amurka ba tare da an tabbatar da yiyuwarsa a kasa ba, ko kuma samun lamuni kan cewa ba zata sake warware ta ba, dole ne su kasance cikin bukatun kasar Iran. Saboda ba Amurka ba abar amincewa bace.

Tun ranar 1 ga watan Jenerun shekarar da muke ciki ne aka fara tattaunawa kan dagewa Iran takunkuman tattalin arziki a Viennan zagaye na 8, abubuwan da kasar Iran take bukata da sun sami amincewar dukkan wadanda suka rage a cikin yarjejeniyar JCPOA. Amma bangaren Amurka da kuma wasu kasashen Turai suna kawo cikas a ci gaba tattaunawar.

342/