Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Antonio Guterres, ya ce ya damu ainun da karuwar cece-kuce game da yuwuwar aukuwar yaki.
Ya ce jefa bil adama cikin damuwa da wargaza tsaron nahiyar Turai da ma duniya baki daya, abu ne mai matukar tsanani, don haka ba za su amince da irin wannan fito na fito mai hadari ba.
A halin da ake ciki dai shugaban Ukraine Ya Ayyana Ranar Laraba, wadda kafafen yada labarai suka ambato a matsayin ranar da Rasha za ta iya kai wa kasar hari.
342/