Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Alkalan sun yi kira ga shugaban kasar Kais Sa’id da ya janye matakin na sa, kuma ya dawo da hukumar shari’a ta kasar, kana sun sha alwashin kare tsarin shari’a da kundun tsarin mulkin kasar
Anasa bangaren shugaban majalisar Ansa Humaidi shugaban kungiyar alkalai ta kasar yace “ muna kira ga shugaban kasar da ya jenye matakin da ya dauka kuma ya kare kasar daga fadawa cikin rashin tabbas sakamakon mataki mai hadari da ya dauka,
Su dai kungiyoyin suna neman hanyar da za su matsayawa gwamnati ne har sai ta biya musu bukatunsu, zanga-zangar da aka yi a makon jiya ya jawo alkalai da dama kauracewam ayyuka tare da rufe dukkan kofofinsa
342/