8 Faburairu 2022 - 14:07
Kotu A Afrika Ta Kudu Ta Yanke Hukuncin Dauri Kan Wasu Tagwaye A Kasar

Rahotanni daga kasar Afrika ta kudu sun bayyana cewa wato wata kotu ta yanke hukumci kan wasu matasa tagwaye na zaman gidan yari bayan da ta zargesu da Ta’adanci da hannun wajen yunkurin kai hari a ofishin jakadancin Amurka dake birnin Pretoriya da kuma hada kai da kungiyoyin ta’adda masu ikirarin jihadi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Takwagen masu suna Tony Lee thulsie da Brandon le thulsie yan shekaru 28 da haihuwa an kama su ne a watan yulin shekara ta 2016 a kasar Afrika ta kudu, kuma ake ci gaba da tsaresu ,

sai a jiya kotun dake zamanta a birnin Johannesburg ta yanke hukumci shekaru 11 a gidan yari kan tony da kuma shekaru 8 kan barando, bayan da suka amsa laifin da ake zarginsu a wani mataki na sulhu da bangaren masu shiagr da kara

Dukkansu a kama su da laifin kokarin yin tafiya zuwa kasar Siriya domin hadewa da kungiyoyin dake ikirarin jihadi, mai shigar da kara ya fadi cewa an shirya kai harin ne kan ofishin jakadancin Amurka da Birtaniya da rasha ko faransa a birnin peretoriya da wasu cibiyoyin yahudawa .

Tuni dai kasarAmurka a sanya sunayi tagwayen cikin jerin sunayen yan ta’adda a shekara ta 2017.

342/