30 Janairu 2022 - 17:10
​Iran Da Rasha Zasu Kauda Dalar Amurka A Huldarsu Ta Kasuwanci

Shugaban kwamitin hadin guiwa na kasashen Iran da Rasha a majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa kasashen biyu sun cimma matsaya dangane da makamashi, wato kan yadda za’a habaka hakar men fetur da iskar gas na kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ibrahim Riza’i shugaban kwamatin Iran da Rasha na majalisun dokoki yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa, daga ciki har da fitar da dalar Amurka a matsayin kudaden musaya a tsakaninsu.

Riza’ii ya kara da cewa a halin yanzu harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen yankin Eurasia ya kai dalar Amurka biliyon $300, idan Iran ta sami ko kashi 10% na wannan harkokin kasuwanci zata sami alkhairi da yawa.

A makon da ya gabata ne shugaban kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, inda kasashen biyu suka kulla yarjeniyoyi da dama.

342/