25 Janairu 2022 - 19:25
Sojoji Sun Kwace Mulki A kasar Borkina Faso

Rahotanni sun nuna cewa sojojin da ke adawa da gwamnati a Borkina Faso sun tabbatar da karbe iko da kasar , kuma sun sanar da rusa majalisar dokokin kasar. A cikin Wata Sanarwar da sojojin suka fitar dake dauke da sa hannun kanar Henri Sandaogo Damiba, da ake ganin shi ne ya jagoranci juyin mulkin an umarci a rufe dukkan iyakokin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tun da fari wasu dakarun kasar ta Afirka ta Yamma sun nemi a kori wasu manyan jami'an soja da kuma samar da ƙarin kayan aiki don yakar masu iƙirarin jihadi da suka Addabi kasar.

An ji karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa da kuma wasu barikin soja tun a ranar Lahadi da ta gabata da dare a Ouagadougou babban birnin ƙasar.

A “yan kwanakin nan sojojin sun musanta labarin yunkurin juyin mulki ko kuma cewa kama shugaban ƙasar, amma kuma a yanzu kusan ta tabbata cewa sun yi juyin mulki ne .

Yanzu haka dai ana tsare da Shugaba Kabore ne a wani sansanin soja. kuma sojoji sun kewaye gidan talabijin na gwamnatin kasar.

342/