Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya nakalto Imam Khamina'i yana fadin haka ne a jiya Lahadi a lokacinda yake jawabi ga mawakan yabon iyalan gidan manzon All...(s) a dai dai ranar haihuwar diyar manzon All..(s) tsarkakakkiya, da kuma na jikinta kuma wanda ya assasa Jumhuriyarn musulunici ta Iran Imam Khomani (q)..
Imam Khamina’i ya kawo ayoyin alkur’ani da hadisan manzon Alla..(s) wadanda suka nuna matsayinta, wadanda suka hada da ayar mubahala, aya ta tsarkakewa, da na suratu hal’ata da sauransu.
An haife Fatimah (s) ne a ranar 20 ga watan Jamada Thani a shekara 5 bayan fara annabci a birnin Makka. Kuma ita da mahaifiyarta Khadiza diyar Khuwilid matar manzon All..(s) ta farko ko mahaifiyan dukkan yayanta in banda Ibrahim na daga cikin matan da All..ya fifita a kan sauran mata a duniya da lahira.
Daga daga cikin wadanda All..ya tsarkaka daga daudar zunubi a cikin al-ummar manzon All..(s) . Sannan itace mahaifiway shuwagabanni wasiyan manzon All..(s) 11 a bayan mijinta Aliyu dan Abitalib (a).
342/